Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi maraba da amincewar Majalisar Dattawan Najeriya da Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki da ke neman kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa wannan gyara zai taimaka wa jihohi wajen kare al’ummarsu yadda ya kamata, musamman Kiristocin da ake tsanantawa.
Moore, wanda ke wakiltar Mazabar 2 ta Jihar West Virginia a Majalisar Wakilan Amurka, ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.
Martaninsa ya biyo bayan amincewar Majalisar Dattawa da kudirin da ke neman rarraba ikon aikin ‘yan sanda ta hanyar bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sandansu tare da ci gaba da kasancewar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kasa.
Moore, wanda a baya ya taba yin magana kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya, ya ce wannan gyara na daga cikin abubuwan da ya dade yana kira a kai a bainar jama’a da kuma a sirrance.
Ya ce: “Na ji dadi da ganin Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar kafa rundunonin ‘yan sanda na jihohi — wani gyara da na dade ina kira a kai a fili da kuma a bayan fage tun lokacin da na fara bincike kan abin da na bayyana a matsayin kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
“Ba zan iya bayyana muhimmancin wannan doka da za ta bai wa jihohi damar kare al’ummarsu da kansu tare da rage dogaro da masu yanke hukunci a Abuja ba. Wannan mataki yana da matukar muhimmanci wajen kare Kiristocin da ake tsanantawa da kuma magance matsalar rashin tsaro.”
Dan majalisar na Amurka ya kuma yabawa Shugaba Bola Tinubu kan goyon bayan da ya ba wa kudirin, amma ya jaddada cewa har yanzu gyaran kundin tsarin mulkin zai bukaci amincewar akalla kashi biyu bisa uku na Majalisun Dokokin Jihohi kafin ya fara aiki a hukumance.