Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi hukumomin Saudiyya da zartar da hukuncin kisa kan wasu ƴan ƙasar Habasha biyar bisa zargin safarar ƙwayoyi, ba tare da bin cikakkun ka'idojin shari'a ba.
A cewar ƙungiyar, an yanke hukuncin ne bayan shari'o'in da ta ce sun gudana cikin gaggawa, inda a wasu lokutan zaman kotun bai wuce ƴan mintuna ba, ba tare da waɗanda ake tuhuma sun samu lauyoyin da za su kare su ko kuma masu fassara ba.
HRW ta bayyana cewa kisan da aka aiwatar a ranar Litinin ya sa adadin ƴan Habasha da aka kashe a Saudiyya a bana ya kai 17, tare da gargadin cewa har yanzu wasu da dama na fuskantar barazanar irin wannan hukunci.
Sai dai hukumomin Saudiyya sun ce an kama mutanen ne da laifin safarar abin da suka bayyana a matsayin "ganye", kuma sun ce an aiwatar da hukuncin ne domin ya zama darasi ga sauran masu aikata irin waɗannan laifuffuka.