Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Iran ta kulla yarjejeniya da China domin sayen makaman kare sararin samaniya da ake harbawa daga kafaɗa, tsakanin guda 300 zuwa 400.
Majiyoyi uku da ke da masaniya kan yarjejeniyar sun shaida wa Reuters cewa ana sa ran Iran za ta fara karɓar kason farko na makaman cikin 'yan makonni masu zuwa.
A cewar majiyoyin, darajar kwangilar ta kai tsakanin dala miliyan 60 zuwa 70, kuma ana kallonta a matsayin wani muhimmin mataki na Iran wajen ƙarfafa kariyarta daga hare-haren jiragen sama.
Sai dai wasu majiyoyin sun bayyana cewa duk da an rattaba hannu kan yarjejeniyar, har yanzu akwai yiwuwar sauye-sauye kan jadawalin jigilar makaman, adadin da za a kai, da kuma wasu bayanan aiwatar da kwangilar.
Rahoton ya ƙara da cewa bisa tsarin da ɓangarorin biyu suka amince da shi, za a fara jigilar makaman ne ta jirgin sama daga birnin Urumqi da ke yammacin China, kafin daga bisani a bi ta ƙasar Pakistan zuwa Iran.
Haka kuma, wata majiya daga ɓangaren tsaron Turai ta shaida wa Reuters cewa jami'an ƙasarta suna sane da yarjejeniyoyin sayar wa Iran makaman da kamfanonin China ke ƙerawa.