Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na gudanar da ayyukanta cikin adalci tare da bin tanade-tanaden doka, yana mai musanta zarge-zargen nuna son kai da ake yi wa hukumar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin Archbishop Matthew Ndagoso a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewarsa, INEC ba ta nuna son kai ko tsoratar da kowa wajen gudanar da zaɓe. Ya ƙara da cewa korafe-korafen da jam'iyyun adawa ke yi na iya kasancewa sakamakon gazawarsu wajen tsara dabarun siyasa.
"INEC ba ta nuna son kai, ba ta taɓa tsoratar da kowa ba. Idan ƴan adawa na ƙorafi, watakila suna zargin kansu ne da kuma rashin shirin da suka yi," in ji Shugaba Tinubu.
A baya-bayan nan dai jam'iyyun adawa sun rika zargin INEC da nuna goyon baya ga jam'iyyar APC mai mulki, lamarin da ya haifar da kiraye-kirayen a sauya shugabancin hukumar. Sai dai Tinubu ya jaddada cewa hukumar na gudanar da aikinta bisa tanadin doka.