Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulki da ke neman samar da rundunonin ƴansandan jihohi a faɗin ƙasar, wani mataki da ake ganin zai kawo babban sauyi a tsarin tsaron Najeriya.
Amincewar ta biyo bayan doguwar muhawara da aka shafe shekaru ana yi kan buƙatar samar da ƴansandan jihohi domin taimakawa wajen magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa sanatoci sun yi nazari kan tanade-tanaden ƙudirin kafin fiye da kashi biyu bisa uku na mambobin majalisar su kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar ƙudirin a zaman majalisar na ranar Laraba bayan samun goyon bayan mafi rinjayen sanatoci.
Ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden ƙudirin shi ne bai wa gwamnonin jihohi damar naɗa kwamishinonin ƴansandan jihohinsu, bayan tantancewa da amincewar majalisun dokokin jihohi.
Zaman majalisar ya samu halartar wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnatin tarayya, waɗanda suka shaida muhawarar da aka yi kan wannan muhimmin ƙudiri da ake sa ran zai sauya fasalin harkokin tsaro a Najeriya.