Girgizar ƙasa mai ƙarfi ta yi sanadin mutuwar mutane 32 a Venezuela

Mutane 32 sun mutu yayin da wasu fiye da 700 suka jikkata sakamakon wasu tagwayen ƙaƙƙarfar girgizar kasa da suka afku a kasar Venezuela.


Masu aikin ceto a yayin neman waɗanda girgizar ƙasa ta rutsa da su a Venezuela.

Masu aikin ceto a yayin neman waɗanda girgizar ƙasa ta rutsa da su a Venezuela. 


Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa ya ga lokacin da wani bene mai hawa 22 ya ruguje gabaɗaya a garin Altamira dake maƙwataka da babban birnin ƙasar, inda mutanen da suka isa wurin ke ta kiran sunayen yan uwansu, a yayin da jami’an agaji ke ƙoƙarin zaƙulo waɗanda ta rutsa da su.


Shugabar rikon ƙwarya ta ƙasar, Delcy Rodriguez, ce ta sanar da hakan a wannan Alhamis yayin wani jawabi da ta yi ga al'ummar ƙasa baki ɗaya.


Rodriguez ta bayyana cewa a halin yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 32 da kuma mutane sama da 700 da suka jikkata wadanda ke bukatar agajin gaggawa.




Ta kara da cewa har yanzu gwamnati ba ta sami cikakkun alkaluma ba game da yankin La Guaira, wanda ke kusa da babban birnin kasar kuma ake fargabar shi ne yankin da bala'in ya fi shafa mafi muni.


Wannan iftila’i ya jefa kasar cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiya.