A daidai lokacin da daminar bana ke kara kankama, mazauna wasu ƙauyuka 26 da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun bayyana cewa sun shiga cikin matsin rayuwa sakamakon harajin tilas da ‘yan bindiga ke kakabawa kafin a ba su damar zuwa gonakinsu.
Mazauna yankunan sun ce maimakon lokacin damina ya zama lokacin shirin noma da samar da abinci, ya koma lokacin fargaba da neman kuɗin biyan harajin da aka sanya musu.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun sanya kuɗin haraji daga Naira miliyan 4 zuwa 6 ga kowace al’umma, inda aka bai wa ƙauyukan wa’adin kwanaki uku su tattara kuɗin ko kuma a hana su shiga gonakinsu.
Wani mazaunin ƙauyen Dogon Faru, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an yi wa jama’a barazanar cewa duk wanda aka samu yana noma ba tare da an biya kuɗin ba zai iya fuskantar sacewa ko ma rasa ransa.
Rahotanni sun kuma nuna cewa gidaje daban-daban suna bayar da gudummawa tsakanin Naira 1,500 zuwa N2,000 domin tara kuɗin, yayin da wasu manoma masu faɗin gona ke biyan har N5,000.