Iyalan marigayi shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a Jihar Benue, Alhaji Ardo Risku, sun bayyana cewa har yanzu ba su samu wata tuntuɓa daga gwamnati ba tun bayan rasuwarsa.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yan sandan jihar ta sanar da kama mutane 10 da ake zargi da hannu a harin da ya yi sanadin mutuwar marigayin da wasu mutum uku.
Iyalan sun ce suna fatan gwamnati za ta sanar da su irin matakan da ake ɗauka yayin da bincike ke ci gaba. A nata bangaren, gwamnatin jihar Benue ta yi Allah wadai da lamarin tare da bayyana cewa an fara bincike.
Jihar Benue na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, kuma hukumomi sun ce suna ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar.