Wata ƙungiya mai rajin sauye-sauye a harkokin shugabanci ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, inda ta ƙalubalanci sahihancin wasu takardun karatu da aka ce Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar wa Hukumar INEC.

A cikin ƙarar, ƙungiyar ta kuma yi wasu zarge-zarge da suka shafi tarihin karatun shugaban, tana neman kotu ta duba batun.

Har yanzu dai waɗannan zarge-zarge ba su tabbatar ba, kuma shari'ar na gaban kotu. Ba a yanke hukunci kan lamarin ba.