Rundunar sojin Mali ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar daƙile jerin hare-haren da wasu mahara suka kai a sassa daban-daban na ƙasar, tare da kashe da dama daga cikinsu.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa bayan farmakin da sojoji suka kai domin murƙushe maharan.
A cewar rundunar, an kai hare-haren ne a birane biyar da suka haɗa da Alguel-Hoc, Anéfis da Gao a arewacin ƙasar, Kenioroba da ke kudancin Bamako, da kuma Sévaré da ke tsakiyar Mali.
Sanarwar ta ce a birnin Sévaré, sojoji sun kashe mayaƙa 20, yayin da aka kashe wasu shida a Gao.
Sai dai rundunar ta bayyana cewa ta rasa soja guda ɗaya, yayin da wasu huɗu suka jikkata a yayin fafatawar.
A halin da ake ciki, ƙungiyar ƴan awaren Azawad Liberation Front (FLA) ta ɗauki alhakin kai hare-haren, lamarin da ke nuna ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro da Mali ke fuskanta.