Mahukunta kasar ta Cango sun ce mutane 80 ne aka iya tseratarwa zu yanzu.

Ana ci gaba da bincike da sa ran ko za a samu wasu da rai bayan wannan haɗari,inda ake kyautata zaton hakan a cewar wani jami'in Red Cross a yankin.


Kungiyoyin ceto sun ci gaba da bincike a bakin kogin a jiya Asabar,suna neman wadanda suka tsira ko kuma gawarwwaki.


A cewar mai kula da yankin Ilebo, François Kabula, sama da mutane 200 ne ke cikin jirgin ruwan, wanda ke tafiya daga tashar jiragen ruwa ta Kalina zuwa Ilebo, a lardin Sankuru. Daga cikin fasinjojin akwai dalibai da yawa da suka dawo gida bayan jarrabawar karshen shekara.


A cewar wasu majiyoyi na gida jirgin ya bar tashar jiragen ruwa da daddare don guje wa binciken tsaro, duk da cewa ya cika da fasinjoji da kaya.