Ƙungiyar kare haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana cewa ba ta amince da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke hukuncin da ya bai wa ɗalibai mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantar International School, Jami'ar Ibadan (ISI).
A cikin wata sanarwa, MURIC ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli, tana mai cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ya ƙunshi kura-kurai na shari'a. Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta riga ta shigar da takardar ɗaukaka ƙara tare da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na ƙarshe.
Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke da rinjayen alkalai biyu kan ɗaya, inda ta ce makarantar ISI makaranta ce mai zaman kanta (private school), don haka hukuncin Kotun Koli da ya amince da sanya hijabi a makarantun gwamnati ba ya shafarta. Sai dai ɗaya daga cikin alkalan ya yi sabanin ra'ayi, yana goyon bayan hukuncin babbar kotun Oyo da ta bai wa ɗaliban damar sanya hijabi.
MURIC ta jaddada cewa za ta ci gaba da fafutukar shari'ar har zuwa Kotun Koli domin neman a sake duba hukuncin, tana mai cewa har yanzu batun bai zo ƙarshe ba.