Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar da cewa dakarun soji na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto domin kuɓutar da ɗalibai 39 da malamai bakwai da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo.

Janar Shaibu ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a birnin Fatakwal, Jihar Rivers, a yayin bukukuwan Ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2026.

An sace ɗaliban da malamansu ne a ranar 15 ga Mayu, 2026, daga makarantu uku da ke Ƙaramar Hukumar Orire a Jihar Oyo.

Ya ce jami'an tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto waɗanda aka sace, yana mai bayyana cewa alamun da ake da su sun nuna ana samun ci gaba a aikin.

"Har yanzu muna ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban, kuma bisa ga bayanan da muke da su, muna da kyakkyawan fata cewa za mu yi nasara," in ji shi.

Babban Hafsan Sojin ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa dakarun za su yi nasarar ceto dukkan waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da mayar da su hannun iyalansu.