Ƙungiyar Hamas ta sanar da rusa kwamitin da ke kula da harkokin gwamnatin Gaza, a wani mataki da ake kallon zai ba da damar kafa gwamnatin farar hula domin tafiyar da harkokin yau da kullum a yankin.

A cikin wata sanarwa, Hamas ta ce shugaban kwamitin gaggawa na gwamnatin, Mohammed Fara, ya miƙa takardar murabus ɗinsa, tare da amincewa da rusa kwamitin baki ɗaya. Ta ce an ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa miƙa alhakin gudanar da ayyukan gwamnati ga sabon Kwamitin Kula da Gudanar da Gaza.

Hamas ta karɓi iko da Zirin Gaza tun a shekarar 2007 bayan rikicin da ta yi da ƙungiyar Fatah, shekara guda bayan nasarar da ta samu a zaɓen majalisar dokokin Falasɗinawa na shekarar 2006.

Tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila da aka cimma a watan Oktoban bara, Hamas ta sha bayyana cewa a shirye take ta janye daga gudanar da harkokin yau da kullum na Gaza. Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya kan batun makaman mayaƙanta da kuma yadda za a tsara harkokin tsaro a yankin ba.

Mai magana da yawun Hamas ya ce rusa kwamitin na daga cikin matakan da ƙungiyar ke ɗauka domin kawar da hujjojin da Isra'ila ke amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan mataki na iya zama wata muhimmiyar hanya ta buɗe ƙofa ga kafa gwamnatin farar hula da za ta jagoranci gudanar da harkokin Gaza a nan gaba, idan aka samu cikakkiyar yarjejeniya tsakanin bangarorin da abin ya shafa.