Gwamnatin Tanzaniya ta tura dakarun soji da jami’an ‘yansanda zuwa manyan biranen ƙasar gabanin wata zanga-zangar ƙasa da aka shirya gudanarwa ranar Talata, domin neman sauye-sauyen dimokuraɗiyya da kuma adalci kan zaɓen shekarar 2025 da ake takaddama a kansa.
Mahukunta sun dakatar da duk wasu tarukan siyasa tun daga ranar 26 ga Yuni, inda suka bayyana cewa matakin na da nufin tabbatar da tsaro. Sai dai ‘yan adawa sun yi Allah-wadai da wannan mataki, suna mai cewa yana tauye ‘yancin jama’a da kuma hana gudanar da harkokin siyasa cikin ‘yanci.
Jami’an tsaro sun ce sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu na shirin amfani da zanga-zangar wajen tayar da tarzoma da aikata ta’addanci. Haka kuma, rundunar sojin ƙasar ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da duk wani yunkuri da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.
Rikicin siyasar ya samo asali ne bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2025, wanda ya haifar da zanga-zanga mai ƙarfi da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 500, a cewar wani kwamitin bincike na gwamnati.
A gefe guda, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da jam’iyyun adawa na ci gaba da zargin gwamnati da ƙuntata fagen siyasa. Sai dai gwamnati ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa matakan tsaron da ta ɗauka na wucin gadi ne kuma an yi su ne domin kare lafiyar ƙasa da al’ummarta.