Mutum huɗu sun rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Maikujera da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta ce maharan sun kutsa ƙauyen ne suna harbe-harbe, inda suka yi garkuwa da mutane tare da satar dabbobi kafin jami’an tsaro su isa wurin.
A cewar rundunar, bayan samun kiran gaggawa, jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar dakarun soji sun bazama yankin, inda suka toshe hanyoyin da ake zargin maharan za su bi wajen tserewa da mutanen da suka sace da kuma dabbobin da suka kwashe.
Lamarin ya rikide zuwa musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindigar, abin da ya tilasta wa maharan tserewa cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su da kuma dabbobin da suka sace.
Rundunar ta bayyana cewa an yi nasarar kuɓutar da mutum 32 ba tare da sun ji rauni ba. Waɗanda aka ceto sun haɗa da maza shida da mata 26, inda mafi yawansu yara ne.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto, Hayatu Hassan Shaffa, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar maharan domin cafke su da gurfanar da su a gaban kuliya.