Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da zaɓen Mista Jerry Adams a matsayin mataimakinsa a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan shawarwari da addu’o’i, yana mai bayyana cewa zaɓin ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta haɗin kai, adalci da bai wa kowane ɗan jihar damar samun wakilci ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da ci gaba a dukkan ƙananan hukumomin jihar, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomin Kaduna.
Ya kuma bayyana Jerry Adams a matsayin gogaggen jami’in gwamnati kuma ƙwararren masani a harkokin haraji, yana mai cewa mutum ne mai gaskiya, ƙwazo da kishin zaman lafiya, wanda zai taimaka wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gina Kaduna mai haɗin kai da ci gaba.