Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gudanar da tattaunawa ta wayar tarho daban-daban da takwarorinsa na Oman da Saudiyya domin duba halin da ake ciki a yankin da kuma hanyoyin rage tashin hankali.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a mashigar ruwan Hormuz, tare da ƙoƙarin diflomasiyya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A baya-bayan nan, Iran da Oman sun gudanar da tattaunawa mai zurfi ta tsawon kwanaki biyu, wadda ta zo daidai da dakatar da hare-haren sojin Amurka. Sai dai, jami’in Iran Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa ƙasar ba ta amince da tayin da Oman ta gabatar a yayin tattaunawar ba.
A wani ɓangaren kuma, tattaunawar Iran da Saudiyya ta zo ne bayan da Saudiyya ta sanar cewa ta kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da aka harba daga Iraq zuwa cikin ƙasarta.
Haka kuma, takun saƙa tsakanin Saudiyya da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya ƙara tsananta a cikin 'yan kwanakin nan, lamarin da ke ƙara tayar da hankali kan tsaro da zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.