Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana cewa ba za ta sake ƙara wa’adin rijistar masu zaɓe ba, duk da kiraye-kirayen da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula suka yi na a bai wa ƙarin mutane damar yin rajista.
Mataimakin Daraktan Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama'a na INEC, Wilfred Ifogah, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Ifogah ya ce dole ne hukumar ta kawo ƙarshen aikin rajistar a wannan lokaci, yana mai cewa waɗanda ba su samu damar kammala rajistarsu ba su yi haƙuri, domin a halin yanzu babu shirin ƙara wa’adin.
Ya tuna cewa INEC ta riga ta ƙara wa’adin rajistar da makonni biyu kafin daga bisani ta rufe aikin a ranar Lahadi.
A cewarsa, ƙarin wa’adin da aka bayar tun farko ya ƙara wa hukumar nauyin kammala shirye-shiryen tattarawa da tantance bayanan masu rajista kafin babban zaɓen shekara mai zuwa.
Ya ƙara da cewa, bisa jadawalin ayyukan INEC, ana buƙatar sama da kwanaki 75 bayan rufe rajista domin tattarawa, tantancewa da shirya cikakken kundin rajistar masu zaɓe kafin gudanar da zaɓe.