Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Abdullahi Gali Shitu, wanda aka fi sani da Comrade Abdullahi Gali Basaf, ya koma sana’arsa ta dinki bayan watanni da kotu ta tsige shi daga mukaminsa.
Basaf, wanda ya jagoranci ƙaramar hukumar har zuwa watan Maris na 2026, ya ce komawarsa sana’ar dinki na da nufin nuna cewa siyasa ba sana’a ce ta dindindin ba, kuma bai kamata ta zama kaɗai hanyar samun abin rayuwa ba.
Da yake zantawa da Daily Trust a ranar Laraba, Basaf ya ce ya dace ‘yan siyasa su kasance da wata sana’a ko hanyar samun kuɗi mai ɗorewa, tare da kallon riƙe muƙamin gwamnati a matsayin dama ta yi wa al’umma hidima.
A cewarsa, sana’ar dinki ce ta kasance babbar hanyar samun kuɗaɗensa fiye da shekara goma, har ma ta taimaka masa wajen tafiyar da harkokin siyasa da yaƙin neman zaɓensa.
“Dinki ba ƙaramin sana’a ba ne. Babbar sana’a ce da ke ciyar da mutane. Hatta a siyasa, sana’ata ta taimaka min wajen ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓe da sauran ayyukan siyasa. Da ba ita ba, da wuya in ci gaba da harkokin siyasa,” in ji shi.
A halin yanzu, Basaf na da shagon dinki a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda yake horar da kimanin matasa 20 masu koyon sana’ar.
Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya bunƙasa sana’ar zuwa matakin kafa kamfanin kera tufafi da zai samar wa akalla mutane 50 ayyukan yi domin ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.
Basaf ya kuma shawarci matasa da su rungumi koyon sana’o’in hannu maimakon dogaro da siyasa ko neman aikin gwamnati kaɗai.
“Saƙona ga matasa shi ne kada su raina sana’a. Su darajanta ta kuma su yi ƙoƙarin inganta ta,” in ji shi.
Ya jaddada cewa sana’a ta fi siyasa tabbaci, domin siyasa na iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci.
“Ku fi daraja sana’arku fiye da siyasa, domin ita ce za ta riƙe ku tare da ba ku damar tallafa wa harkokinku na siyasa,” ya ƙara da cewa.
Duk da kasancewarsa mai digirin farko da na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa, Basaf ya ce ya zaɓi komawa dinki ne saboda sana’ar ce ta fi burge shi tun farko, kuma yana da niyyar faɗaɗa ta zuwa babban kamfani.
Kafin ya zama Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Basaf ne ya kafa dandalin Kwankwasiyya Reporters a shekarar 2015. Ya kuma taɓa zama shugaban jam’iyyar Alliance National Party (ANP) a Jihar Kano, ya tsaya takarar Sanata a shekarar 2019, sannan daga baya ya koma jam’iyyar NNPP, inda ya yi aiki a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai.
Ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso a shekarar 2024, amma wa’adinsa ya ƙare a watan Maris na 2026 bayan Babbar Kotun Jihar Kano ta soke Takardar Shaidar Cin Zaɓensa tare da ayyana Ali Musa, wanda aka fi sani da Hardworker, a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar.
Sai dai Basaf ya ce duk da komawarsa sana’ar dinki, bai yi watsi da siyasa ba, domin zai ci gaba da taka rawa a harkokin siyasar Najeriya.
“Siyasa na iya canzawa cikin dare ɗaya. Kana kan mulki yau, gobe kuma ka fita. Amma sana’a tana nan, tana ciyar da kai, tana kula da iyalinka, kuma tana ba ka damar taimakon wasu,” in ji Basaf.