Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ba ta nuna son kai wajen gudanar da ayyukanta, yana mai jaddada cewa hukumar na aiki ne bisa tanadin doka.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin da yake karɓar jagororin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Archbishop Matthew Ndagoso, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Jawabin na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ke fuskantar zarge-zargen nuna son kai daga wasu jam’iyyun adawa, waɗanda suka zargi hukumar da fifita jam’iyyar APC mai mulki a wasu matakan da take ɗauka.
Wasu daga cikin masu sukar hukumar sun kuma yi kira ga shugaban INEC da ya sauka daga muƙaminsa.
Sai dai Tinubu ya yi watsi da waɗannan zarge-zarge, yana mai cewa hukumar ba ta taɓa tsoratar da kowace jam’iyyar siyasa ba, kuma tana gudanar da ayyukanta cikin adalci.
“INEC ba ta nuna son kai, ba ta taɓa tsoratar da kowa ba. Idan ’yan adawa na ƙorafi, watakila suna zargin kansu ne da kuma rashin shirin da suka yi,” in ji Shugaba Tinubu.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da mutunta ’yancin hukumomin dimokuraɗiyya tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.