Sama da mutane 55475 ne suka kamu da cutar amai da gudawa, cikin watanni shida a Jihar kano

Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema Labarai, Kan ranar wayar da kai Kan muhimmancin ruwan gishiri da siga a jikin Dan Adam. 


Dr Abubakar ya Kara da cewa cikin watanni shida Gwamnantin Kano ta gano sama da mutane 55574 dake sukayi Sama da cutar amai da gudawa, kuma tuni Gwamnati ta dauki matakan gaggawa na samar magunguna ciki har da ruwan gishiri da suga dan kare yara daga mutuwa bisa karancin ruwa a jikinsu. 


Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya ce Gwamnatin Kano ta Samar ruwa gishiri da siga mai tarin yawa dukan asibitocin jihar. 


A yayin amsa tambayar da wakilinmu Adamu Abdullahi ya yi wa kwamishinan kan kalubalen da Mutanen karkara ke fuskanta wajen samun kulafar Lafiya ne, kwamishinan yace Gwamnati ta samar da wani tsari karkashin hukumar Samar magunguna ta Jihar Kano, da zai rika Kai magunguna a lungu da sakunan Jihar da Kwamishinan ya Kira da duk Nisan gari. 


Akwai dai bukatar iyaye suka rika kula da cimakar 'ya 'yansu, musamman ruwansha don kaucewa cututtuka dake adabar Yara a Lokacin damuna.